Sabuwar cutar corona samfarin Omicron zata jefa duniya a cikin matsanancin hali a cewar WHO

0 59

Hukumar lafiya ta duniya WHO tayi gargadin cewa sabuwar cutar corona samfarin Omicron zata jefa duniya a cikin matsanancin hali.

Ta bayyana hakan ne a jiya, inda tace, babu shakka wannan zai haifar matsaloli ga yankuna da dama a duniya.

Shugaban hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan, a lokacin dayake gabatar da jawabinsa, na neman hadin kan duniya domin yaki da wannan cutar.

Tare da kiran kasashen duniya masu karfin tattalin arziki akan su taimakawa matalautan kasashe.

Kafin hakan dai wannan samfarin cutar ta samo asali ne daga kasar Afrika ta kudu a farkon wannan watan, kuma angano cewa tana da  hadari sosai ga al’umma.

Hakanne yasa kasashen Amurka, Birtaniya da tarayya turai, suka haramta zuwa Afrika ta kudu, ko kuma shiga kasashensu.

Hakanne yasa shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya soko wannan matakin da kasashen suka dauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: