Sabuwar Makarantar Karamar Sakandire Muhammad Abubakar Dake Karamar Hukumar Ta Guri Za Ta Fara Aiki A Wannan Watan
Sabuwar makarantar karamar sakandire Muhammad Abubakar dake karamar hukumar ta Guri za ta fara aiki a wannan watan.
Shugaban karamar hukumar Guri, Alhaji Musa Shuaibu Muhammad Guri ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai. Ya ce makarantar ta kunshi ajujuwa shida, na gudanarwa 1 , bandaki da kuma burtsatse. Alhaji Musa Shu
aibu Guri, ya kuma karamar hukumar sa ta bayar da kwangilar yin jinga a Takazza, Garmakuwan Gabas da Garmakuwan Yamma domin kaucewa ambaliyar ruwa.
Ya yi kira da a ci gaba da addu’a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.