Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Ya Isa Birnin Mogadishu Na ƙasar Somaliya
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya isa birnin Mogadishu na ƙasar Somaliya a wata ziyara da ya kai ƙasar dake fama da tashe-tashen hankula daga yan tayar da kayar baya da kuma rikicin sauyin yanayi.
Ministan harkokin wajen Somaliya Abshir Omar Huruse ya tarbi Guterres a filin jiragen sama na babban birnin kasar kamar yadda ya yada wasu hotuna a shafin sa na Tweeter a yau.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce ana sa ran babban sakataren majalisar zai yi jawabi kan ƙaruwar taɓarɓarewar ayyukan jin ƙai a ƙasar, tare da nuna goyon bayansa ga ƙasar a yaƙin da take yi da ‘yan ta’adda.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa kusan mutane miliyan takwas ne ke buƙatar taimakon jin-ƙai, kuma mafi yawan mutanen na dab da faɗawa ƙangin yunwa bayan damina biyar a jere ba tare da samun isasshen ruwan sama ba.
Gwamnatin ƙasar dai na samun nasara a yaƙin da take yi da ‘yan ta’addan al-Shabaab, musamman a tsakiyar ƙasar. Gutterez zai gana da shugabannin ƙasar, ana kuma sa ran fitar da sanarwar bayan ganawar daga fadar gwamnatin ƙasar.