Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhamamdu Buhari akan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya wanke shugaban kasa Muhammadu Buhari daga sukar da ake masa na cewa salon mulkin sa ya taimaka wajen raba kan al’ummar kasar nan.

Kafin hakan dai Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa limamin cocin Katolika na darikar Sokoto, Matthew Kukah, a jiya, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da kakkausar murya kan rashin tsaro, cin hanci da rashawa da kuma rarrabuwar kawunan yan kasar nan.

Kukah ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na Easter mai taken, ‘A gyara al’ummar da ta rushe’

A cewar Bishop din, an lalata kowane fanni na rayuwa a Najeriya yayin da ake cigaba da cin hanci da rashawa.

Anasa martanin mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya ce, abin mamaki ne a ce wadanda suke da laifin haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya, su ne suke zargin shugaban kasar akan irin laifin da suka aikata a baya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: