Sama Da Fararen Hula 50 Ne Suka Mutu A Sudan Yayin Wani Rikici Da Sojin Kasar

0 82

Rikicin madafun iko tsakanin sojojin Sudan da wata fitacciyar rundunar soji ya mamaye kasar, inda aka ce sama da fararen hula 50 ne suka mutu.
Mutane sun yi watsi da harbin bindiga a babban birnin kasar, Khartoum, yayin da dakarun da ke gaba da juna suka yi artabu akan kwace ikon fadar shugaban kasa, da gidan talabijin na gwamnati, da kuma hedkwatar sojoji.
Wata kungiyar likitoci a kasar ta ce mutane 25 da suka hada da fararen hula 17 ne suka mutu a birnin.
Rikicin dai ya barke ne bayan tashe-tashen hankula kan shirin mika mulki ga farar hula.
Dakarun soji da masu adawa da su wato kungiyar RSF, sun yi ikirarin cewa, sun mallaki filin jiragen sama da wasu muhimman wurare a birnin Khartoum, inda aka ci gaba da fada cikin dare.
An ji karar manyan bindigogi a Omdurman da ke kusa da birnin Khartoum da kuma Bahri da ke kusa da su da sanyin safiyar yau. Shaidun gani da ido sun kuma bayar da rahoton cewa, an yi ta harbe-harbe a birnin Port Sudan da ke gabar tekun Red Sea.

Leave a Reply

%d bloggers like this: