Sama da mutane 17,000 sun nemi guraben aikin koyarwa 2,500 a jihar Abia

0 85

Gwamnatin Jihar Abia ta bayyana cewa mutane sama da 17,000 sun nemi guraben aikin koyarwa 2,500 da aka bude.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Prince Okey Kanu, ya ce wadanda aka zaba za su fuskanci jarrabawar kwamfuta da kuma tattaunawa kafin a dauke su aikin.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin Alex Otti na kokarin kara yawan malamai a makarantun jihar domin inganta harkar ilimi.

Sai dai gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana sa ran samun kudin shiga har Naira biliyan 120 daga cikin gida a shekarar nan ta 2025.

Leave a Reply

%d bloggers like this: