Sama da mutane dubu 30 sun tsere daga arewacin ƙasar Kamaru zuwa Chadi biyo bayan rikicin kabilanci

0 118

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu 30 sun tsere daga arewacin kasar Kamaru zuwa makwabciyarta Chadi a wannan makon, biyo bayan rikicin kabilanci da ya yi sanadiyyar rayuka akalla 22.

Rikicin ya barke ne a karshen mako a wani gari da ke kan iyaka, bayan sabanin da aka samu tsakanin makiyaya da manoma da masu kamun kifi kan madatsar ruwa.

Kana daga bisani rikicin ya ta’azzara har zuwa kauyuka makwabta, inda aka kone akalla kauyuka 10.

Majalisar Dinkin Duniya tace kashi 1 cikin 3 na mutanen da suka tsere zuwa Chadi mata ne, wadanda akasari ke dauke da juna biyu, da kuma kananan yara.

Ko a watan Agusta sai da aka samu makamancin wannan rikici a arewacin kasar Kamaru inda mutane 40 suka mutu, sannan dubbai suka tsere zuwa garuruwan da ke kan iyaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: