Sama da mutane miliyan biyu ne zasu rasa matsugunansu a Arewa maso Gabashin kasar nan

0 111

Sabuwar shugabar tawagar Tarayyar Turai ta ECOWAS, Samuela Isopi, ta ce sama da mutane miliyan biyu ne zasu rasa matsugunansu a Arewa maso Gabashin kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a Abuja ya rawaito cewa jami’ar ta bayyana haka ne a jiya a wajen bikin kaddamar da fara wani shirin fim, wanda kungiyar Tarayyar Turai ta dauki nauyi.

Ta kara da cewa Tarayyar Turai a matsayinta na abokiyar huldar Najeriya a fannin raya kasa, ta bayar da kudi kimanin Euro miliyan 130 a cikin shekaru hudu da suka gabata don taimakawa gwamnatin tarayya wajen sake ginawa, gyara da kuma kokarin samar da zaman lafiya.

Ita ma a nata jawabin, ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta amince da matsayar wakiliyar Tarayyar Turai game da mahimmancin samar da abinci, inda ta ce ma’aikatarta, ta hannun hukumar raya yankin arewa maso gabas na magance wannan batu da gaske.

Leave a Reply

%d bloggers like this: