Sama da yara miliyan 18.3 ne ba sa zuwa makaranta – UNICEF

0 168

A yayin da ake shagulgulan Ranar Yara ta Duniya a bana, masana da kungiyoyin farar hula sun nuna damuwa matuka dangane da karancin yara da ke samun ilimi a Najeriya, inda rahoton UNICEF ke nuna cewa, sama da yara miliyan 18.3 ba sa zuwa makaranta.

Farfesa Lai Olurode da shugaban kungiyar malamai ta NUT a Jihar Oyo, Raji Oladimeji, sun bukaci gwamnati da ta dawo da tsarin ilimi kyauta kuma tilas, da gyara gine-ginen makarantu da tallafa wa iyaye marasa galihu.

Hukumomi da masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa rashin ilimi ga yara na nufin lalacewar makomar kasa, inda suka bukaci samun hadin gwiwa daga gwamnati, kungiyoyin addini da kamfanoni masu zaman kansu don ceto wadannan yara da ba su damar cika burinsu.

Leave a Reply