Shugaban majalissar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bayyana dalilan da gwamnatin tarayya take da shi don cigaba da ciyo bashi don daukar nauyin muhimman ayyuka a kasa.

Shugaban majalisar yana gani ba’abu ne mai yiyuwa ba, ga gwamnati ta karawa mutane kudaden haraji ta fuskar halin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.

Ahmad Lawan ya yi wannan bayanin a jiya al’hamis ya yin ganawa da manema labaran fadar shugabankasa, bayan wata ganawar sirri da sukayi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Ya bada tabbacin cewa majalissar dokokin kasa zata bawa majalissu iziki don zartar da rancen daukar nauyin dokar kasafin kudin bana kafin ta fara hutun watan Yuli.

Ahmad Lawan ya ce za’a sake nanata dokar a shekarar 2021kafin su tafi hutun don sayo magani cutar Corona da kuma kayan aikin sojoji don magance matsalar tsaron da ta addabi kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: