Sanata Ahmad Lawan ya kaddamar da kwamitin wucin gadi domin binciken rashin bin dokar masana’antar man fetur da kuma yarjejeniyar hako mai a Najeriya

0 69

Sanata Ahmad Lawan, a jiya ya kaddamar da kwamitin wucin gadi wanda majalisar ta kafa domin binciken rashin bin dokar masana’antar man fetur da kuma yarjejeniyar hako mai.

Kwamitin mai mutane bakwai yana karkashin jagorancin mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Sabi Aliyu Abdullahi.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Sanata George Sekibo, da Sanata Yahaya Abdullahi, da Sanata Albert Akpan, da Sanata Solomon Adeola, da Sanata Smart Adeyemi da kuma Sanata Aishatu Dahiru.

Da yake kaddamar da kwamitin, shugaban majalisar dattawan ya dorawa mambobin kwamitin daukar wannan aiki a matsayin wani babban yunkurin bincike don gyara kura-kuran da kuma fallasa cin hanci da rashawa.

Majalisar dattawa ce ta kafa kwamitin wucin gadi a zamanta na ranar 22 ga watan Yunin 2022 biyo bayan wani kudiri da Sanata George Thompson Sekibo ya dauki nauyi domin gudanar da bincike kan rashin bin dokokin da ake da su a bangaren harkar mai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: