Sanata Danladi Sankara ya bada gudunmawar Naira Miliyan 20 da buhu 10,000 na shinkafa da kuma sauran kayan tallafi ga mutanen da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa

0 84

Shugaban Kwamatin Yada Labarai da Fadakarwa na Majalisar Dattawa Sanata Danladi Sankara, ya bada gudunmawar Naira Miliyan 20 da Buhu dubu 10,000 na Shinkafa da kuma sauran kayan Tallafi ga mutanen da Iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Jihar nan.

A cewar Sanatan, Kudaden da kuma Kayan Abincin za’a raba su zuwa Kananan Hukumomi 12 da ya ke Wakilta a yankin Jigawa ta Arewa Maso Yamma.

Sanatan ya bada gudunmawar ne a lokacin da ya kai ziyarar duba wuraren da iftila’in ya shafa a jiya.

Danladi Sankara, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu tare da bawa Iyalansu hakurin zure rashin.

Haka kuma ya ce tun da Jimawa ya rubutawa Ministar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma wasikar neman tallafi ga mutanen yankin Jigawa ta Arewa Maso Yamma.

Kazalika, ya ce ambaliyar ruwan ta shafi Kananan Hukumomi 12 na Masarautu 3 da ya ke wakilta wanda suka hada da Gumel, Kazaure da Ringim.

Leave a Reply

%d bloggers like this: