Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a yau ta ayyana Sanata Ibrahim Bomai na jam’iyyar APC a mazabin wanda ya lashe zaben sanatan Yobe ta kudu.
Jami’in hukumar zaber, Dr. Abatcha Melemi na jami’ar tarayya dake Gashuwa, shine ya sanar da sakamakon zaben a Potiskum.
Abatcha Melemi ya bayyana cewa Ibrahim Bomai ya samu kuri’u dubu 69 da 596 inda ya kayar da Halilu Mazagane na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u dubu 68 da 885.
Abatcha Melemi ya cewa Isa Musa na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u dubu 3 da 277 inda yazo na uku.
Da yake jawabi jim kadan bayan ayyana sakamakon, Ibrahim Bomai ya godewa Allah SWT bisa nasarar da ya ba shi.
Hukumar ta INEC ta ayyana zaben ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin wanda bai kammalu ba, bayan soke sakamakon zabe na akwatin zabe ta uku dake Manawaci a karamar hukumar Fika, lamarin da ya jawo gudanar da zaben cike gibin na yau.
- Comments
- Facebook Comments