Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce sanatoci uku daga Jihar Kebbi da ke ƙarƙashin jam’iyyar PDP na dab da sauya sheƙa zuwa APC.
Ganduje ya bayyana hakan bayan wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa tare da Gwamna Nasir Idris da wasu manyan ‘yan siyasa daga jihar.
Ya ce tuni an cimma matsaya a boye tsakanin manyan ‘yan siyasa na jihar, kuma shugaban ƙasa ya amince da wannan mataki, wanda ake sa ran zai tabbata a ranar Talata a zauren Majalisar Dattawa.
Ganduje ya kara da cewa matakin yana da nasaba da dabarun siyasa na jam’iyyar domin ƙarfafa yawan mambobinta da tabbatar da ingancin shugabanci a matakin ƙasa.