Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmed Bola Tinubu na shugabancin kasa.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar wata tawagar kungiyoyin Arewa masu goyon bayan takarar shugabancin kasar Tinubu da suka kai masa ziyara a fadarsa da ke Katsina a jiya.

A cewarsa, Tinubu mutum ne da zai iya ceto yan Najeriya daga matsalolin tsaro, tattalin arziki da zamantakewa.

Sarkin ya ce ya san Tinubu tsawon shekaru saboda yana da kusanci da mahaifin sa, Marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Muhammad Kabir Usman

Sarkin ya bayyana cewa biyo bayan matsalolin tsaro da suke cigaba da addabar Arewacin Najeriya, akwai bukatar a samu mutumin da zai ceto yankin daga matsalolin da suke addabar kasar nan.

Tunda farko, Shugaban tawagar, tsohon Dan majalisar Dattawa, Sanata Abu Ibrahim ya shaidawa Sarkin cewa suna zagayawa ne domin neman hadin kan yan Najeriya su goyi bayan abokinsu da suke koyi da shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: