Mai martaba Sarkin Hadejia kuma shugaban majalissar sarakunan jihar Jigawa Dr Adamu Abubakar Maje ya kaddamar da zagayen farko na allurer rigakafin shan inna ta bana a Tafkin Tumballe dake karamar hukumar Mallam Madori.

A jawabinsa mai martaba sarki ya hori iyayen yara dasu tabbatar an yiwa yayansu rigakafin saboda muhimmancinsa.

A jawabinsa shugaban Karamar Hukumar Mallam Madori, Alhaji Hussain Umar BK ya bukaci mai martaba sarki daya gabatar musu da bukatar gyaran tafkin na Tumballe ga gwamnatin jiha.

Yace yin hakan zai taimaka wajen magance matsalar dake damun alummar yankin.

A jawabinsa, jamiin hukumar lafiya matakin farko na yankin Hamza Bello ya yaba da kokarin shugaban karamar hukumar a duk lokacin zagayen rigakafin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: