Sarkin Hadejia ya shawarci Sabon Kwamandan NDLEA na shiyyar Hadejia

0 252

Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje CON, ya shawarci Sabon Kwamandan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi na Shiyar Hadejia ya ninka kokarin sa domin dakile shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Dr Abubakar Maje, ya bada shawarar ne a lokacin da sabon Kwamandan Shiyar ya kawo masa ziyara a fadar sa.

Sarkin ya ce dole Ofishin ya kara ninka kokarinsa, tare da sanya idanu domin dakile matsalar shaye-shayen da ta zama ruwan dare cikin Al’umma.

Haka kuma Sarkin ya bukaci Kwamandan hukumar ya kasance mai jajircewa akan aikin sa, tare da hukunta duk wanda aka kama.

Kazalika, Mai Martaba Sarkin, ya bada tabbacin cewa Majalisar sa, bazata shiga hurumin aikin hukumar ta NDLEA ba, inda ya kara da cewa Majalisar zata tallafawa hukumar domin gudanar da ayyukanta.

Tun farko a jawabinsa, Sabon Kwamandan Hukumar NDLEA na shiyar Hadejia Alhaji Bashir Magaji Kazaure, ya ce ya kawo ziyara fadar ne domin neman goyan bayan Majalisar Sarki kan ayyukan hukumar tare da neman Albarka.

Shugaban ya ce daga zuwan sa kawo yanzu, sunyi Nasarar kama Dilolin kwayoyi 120, inda aka gabatar da mutane 80 a gaban Kotu, tare da hukunta mutane 30.

Kazalika, ya ce hukumar sa ta Kasa, tana daukar Ma’aikata dubu 2,000 domin cike gibin Ma’aikatan da hukumar take dasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: