Sarkin kano mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’umarsa da sauran yan Najeriya akan su karbi rigakafin cutar corona, a dai-dai lokacin da yanayin hunturu keratowa, yanayin da al’uma suka fi kamuwa da cutukan mura tari wanda ke kara yawan wadanda ke kamuwa da cutar corona cikin sauri.

Sarkin wanda ya bayyana haka ga manema labarai a wata ganawa da yan Jaridu a fadarsa, jim kadan bayan karbar tasa Sabuwar rigakafin, ya shawarci aluma dasu cigaba da kiyaye dokokin cutar wanda suka hada da bada tazara, da nisantar Taruka marasa muhimmanci.

Sarkin ya bukaci iyaye mata,musamman masu juna biyu akan suna amincewa ana musu gwajin domin kare lafiyarsu da abinda suke dauke dashi.

Kazalika sarki Bayero ya jinjinawa kokarin da gomnati keyi wajen dakile yaduwar cutar kwalara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: