Labarai

Sarkin Musulmi ya ce mutuwar matasa 29 a wani hatsarin kwale-kwale da ke karamar hukumar Shagari a Jihar Sakkwato, abin takaici ne.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce mutuwar matasa 29 a wani hatsarin kwale-kwale a kauyen Gidan-Magana da ke karamar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato, abin takaici ne.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana ra’ayinsa ne a jiya a ziyarar jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da jama’a da gwamnatin jihar Sokoto a kan iftila’in da ya afku a ranar Laraba.

Sarkin Musulmin, wanda ya samu wakilcin Sarkin Kabin Yabo, Alhaji Muhammadu Maiturare, ya bayyana lamarin a matsayin kaddara daga Allah madaukakin sarki.

Yanzu haka Sarkin Musulmin yana kasar Saudiyya yana gudanar da Umrah.

Idan dai za a iya tunawa, matasan sun rasa rayukansu ne a ranar Laraba a lokacin da kwale-kwalen da suke tafiya a cikin kogin Shagari domin neman itace ya kife.

Daga cikin wadanda suka mutu, 23 mata ne, 6 maza, yayin da aka ceto mutane shida da ransu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: