Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Kasa, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya umarci Musulmi da su duba jinjirin watan Shawwal na shekarar 1444 bayan Hijira daga yau.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu, a Sokoto.
Sarkin Musulmi ya yi addu’ar Allah SWT ya tallafa wa musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.
Ganin jinjirin wata zai kawo karshen azumin farilla na wata guda da musulmi ke yi a fadin duniya.
Watan Shawwal shi ne wata na 10 a cikin kalandar Musulunci da Musulmi a fadin duniya suke gudanar da bukukuwan Sallah Karama.