Saudiyya ta sanar da buɗe ƙofarta ga masu son zuwa Umarah

0 161

Ma’aikatar Hajji da Umarah ta ƙasar Saudiyya ta sanar da buɗe ƙofarta ga masu son zuwa aikin Umarah na shekarar Hijira ta 1447, wanda zai fara daga ranar Talata, 10 ga Yuni.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa za a fara bayar da takardar izinin Umarah ga ƴan ƙasashen waje daga yau Laraba, 11 ga watan Yuni, ta manhajar “Nusuk”.

Saudiyya ta dakatar da bayar da izinin aikin Umarah a watan Afrilun 2025, sannan ta ayyana 29 ga Afrilu a matsayin rana ta ƙarshe da masu Umarah za su bar ƙasar, gabanin aikin Hajjin shekarar 2025.

Mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida ne suka gudanar da aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an fara shirye-shirye tare da haɗin gwiwa da hukumomi da masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da saukin aiwatar da dukkan matakai da kuma ci gaba da ingantawa na ayyukan ibada.

Haka kuma ta ce ana ci gaba da ƙoƙari wajen fadada ayyukan gwamnati ta tsarin fasahar zamani da kuma wayar da kai a cikin harsuna daban-daban, da kuma samar da ingantattun matakan tsaro da jin dadi ga masu Umarah.

Leave a Reply