Dalilan da yasa Sergio Ramos ya bar kungiyar Real Madrid bayan ya shafe shekaru masu yawa.

0 241

Kyaftin ɗin Real Madrid Sergio Ramos ya yi sanarwar barin ƙungiyar a cikin wani guntun rubutu mai kalmomi biyu “Ina Godiya”, a shafukan sa na sada zumunta.

Aikawa da saƙon cikin ‘yan mintina sama da mutum 500,000 kafin minti 30 sun shiga shafin, daga masu jimami, sai masu kukan-zuci, sai kuma masu yi masa fatan alheri.
Ramos ya bar Madrid wata ɗaya bayan tafiyar kociya Zidane.

Har yanzu dai Ramos bai bayyana sunan ƙungiyar za dai koma ba, duk kuwa da tambayoyin da sama da masoyan sa dubban ɗaruruwa su ka yi masa.

A tsawon shekaru 16 da Ramos ya yi a Madrid bayan an saye shi daga Seville FC, ya taimaki ƙungiyar ta ci kofuna 22.

Ya buga wasanni 671 a Madrid, kuma ya ci mata ƙwallaye har 101, duk da kasancewar sa mai tsaron baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: