Sheikh Sani Jingir Na Kungiyar Izala Ya Gargadi Al’ummar Musulmi Da Su Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci A Duk Abin da Suke Yi.

0 227

Shugaban Majalisar Malamai na kasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya gargadi al’ummar Musulmi da su tabbatar da gaskiya da adalci a duk abin da suke yi.

Ya bayar da wannan nasihar ne a wajen rufe lakcocin watan Ramadan karo na 11 da Kwamitin matasa da yada addinin Musulunci na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ya shirya a Masallacin Yantaya da ke Jos, Jihar Filato.

Malamin wanda ya samu wakilcin Sheikh Aliyu Sange, ya ce dole ne daidaikun mutane su tashi tsaye wajen yakar munanan dabi’unsu da kuma kiyaye tsoron Allah SWT a harkokinsu na yau da kullum.

Babban bako mai jawabi, Sheikh Hassan Dikko, ya hori jama’a da su kiyaye maganganunsu a kodayaushe daga cin naman mutane, yada kiyayya da munanan zaton da ke iya yin illa ga dangantaka.

Leave a Reply