Shekarau Ya Samu Sabon Muƙami A Majalisa

0 297

Shugaban Majalisar dattijai na tarayyar Najeriya Sanata Dr Ahmed Lawn ya bayyana sunan Mallam Ibrahim Shekarau a matsayin shugaban kwamitin harkokin hukumomin gwamnati da dukkan ma’aikata na tarayya.

Sunan kwamitin: Establishment and Public Service.

An fadi wannan suna ne cikin sunayen da aka gabatar a yau da rana bayan kammala tantance ministocin kasar da sahalewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada su ba tare da wata tangarda ba.

Majalisar dattijai ta kafa kwamitoci guda 69.
Kwamitin da aka sanya amanarsa a hannun Sanata Ibrahim Shekarau shi ne yake da alhakin kula da tafiyar da duk hukumomin gwamnati da ma’aikatunsu da duk ma’aikatan gwamnatin tarayya. Babban kwamiti ne komai da ruwanka, wanda zai lura da kafa duk wata sabuwar hukuma da sake fasalin tsohuwa.

A wajen saka Sanata Ibrahim Shekarau kan wannan jagoranci Majalisar dattijai ta yi la’akari da kwarewarsa da gogayyarsa da sanin makamar aikin harkar gwamnati da kuma amanarsa da zai rike ta ma’aikatan Najeriya a majalisa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: