‘Shirin aikin tashar wutar lantarki ta Mambila ku dauke shi a matsayin mafarki’ -EFCC

0 93

Kwamitin Wutar Lantarki na Majalisar Dattawa ya bayyana shirin aikin tashar wutar lantarki ta Mambila a matsayin mafarki, duk da kasafin kudin da aka dinga yi mata kowace shekara na biliyoyi.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC take bincike akan aiwatar da aikin.

Tashar wutar lantarki ta Mambila wacce za ta samar da wuta mai karfin megawatt dubu 3 da 50, har yanzu ba a kokarin aikin ta.

Idan aka kammala, ana sa ran za ta zama tashar wutar lantarki mafi girma a kasarnan, kuma daya daga cikin mafiya girma a nahiyar Afrika.

Gwamnatin tarayya ta ware naira miliyan dubu 2 domin aikin tashar ta Mambila a kasafin kudin 2020. Tashar ta samu naira miliyan 425 a bara da miliyan 650 a bana da kuma naira miliyan dubu 1 da miliyan 100 a kasafin kudin badi.

Shugaban kwamitin, Sanata Gabriel Suswam, yace abin takaici ne ace babu wani aikin da aka yi a tashar duk da makudan kudaden da aka kashe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: