Shugaba Buhari na Najeriya ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa don gyaran Najeriya tun daga sanda ya shiga aikin soja.

0 63

Shugaba Buhari na Najeriya ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa don gyaran Najeriya tun daga sanda ya shiga aikin soja.

Maganar tasa wani ɓangare ne na jawabin da ya gabatar da safiyar yau Asabar, 12 ga Yuni, a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya.

Tsohon sojan wanda ya mulki Najeriya a shekarar 1983 ƙarƙashin mulkin soja, ya jaddada jajircewarsa wajen “ɗorewar Najeriya ƙasa ɗaya”.

“A matsayin mu na ƙasa, mun yi nisa daga inda muka faro sannan kuma muna ƙara kusantar inda muka sa gaba cikin sauri,” in ji shi.

“Kawo ƙarshen ƙalubalen da muke fuskanta a yanzu hanya da ya zama mu bi ta a matsayinmu na ƙasa saboda mu farfaɗo da ƙarfinmu. Tun daga ranar da na shiga aikin soja na kasance cikin shirin sadaukar da rayuwata ga Najeriya.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: