Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya kaddamar da kwalbati mai tsayin kilomita 7.6 domin magance zaizayar kasa a karamar hukumar Jama’are ta jihar Bauchi.

Shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin karamar ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Maryam Yalwaji Katagum, yace an gudanar da aikin ne domin dakile wahalhalun da mazauna wajen ke fuskantar.

Shugaba Buhari aiki zai magance babbar matsalar yanayi dake fuskantar mazauna wajen.

Yace gwamnatin tarayya ta gudanar da manyan ayyukan dakile zaizayar kasa a garuruwa da kauyuka dayawa a fadin kasarnan.

Da yake yabawa dan kwangilar saboda ingancin aikin, shugaban kasar ya bukaci mazauna wajen da su tabbatar da sun yi amfani da aikin ta hanyar da ta dace tare da tsare shi daga bata gari.

A nasa jawabin, gwamnan jihar, Bala Abdulkadir Mohammed, ya yabawa shugaban kasa bisa aikin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: