Shugaba Buhari ya amince da kashe kudi naira biliyan 13 da miliyan 300 domin fara shirin ‘Yan Sandan Cikin Al’umma

0 78

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe kudi naira biliyan 13 da miliyan 300 domin fara shirin ‘Yan Sandan Cikin Al’umma a fadin kasarnan.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin bude wani taron bita na kwanaki biyu na bibiyar ayyukan ministoci, wanda aka shirya don tantance cigaban da aka samu don cimma muhimman abubuwan da gwamnatin sa ta sa a gaba, yau a Abuja.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa amincewar na daga cikin matakan karfafa kokarin gwamnati da nufin inganta tsaro a duk fadin kasar.

Ya kuma sanar da cewa an umarci Ma’aikatar Tsaro da ta samar da wani katafaren masana’antar kere kayan soji don kera makamai na cikin gida don biyan bukatun sojojin kasarnan.

Shugaban kasar ya yi bayanin cewa kafa masana’antar zai magance dogaro da Najeriya ke yi kan wasu kasashen don kayan aikin soji da dabarun yaki.

Akan sauran hanyoyin karfafa tsaron kasa, shugaban kasar yace abin farin ciki ne ganin cewa Najeriya ta karbi jiragen saman yaki na Super Tucano guda shida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: