Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake kafa sabon kwamitin gudanarwa na hukumar yada labarai ta kasa (NBC).

Kamar yadda yazo cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun ministan labarai da al’adu, Segun Adeyemi, hakan na zuwa ne sanadiyyar karewar wa’adin aikin kwamitin gudanarwa na hukumar.

Sanarwar ta rawaito ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ambaci sunan Bashir Omolaja Bolarinwa a matsayin shugaban sabon kwamitin gudanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa kwamitin gudanarwa na da wa’adin aiki na shekaru uku.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: