Shugaba Buhari ya amince da wani kwamiti mai lura da sabuwar dokar masana’antar man fetur

0 84

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wani kwamiti da zai kula da yadda ake aiwatar da sabuwar dokar masana’antar man fetur.

Kwamitin gudanarwar na karkashin jagorancin karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva.

Shugaban kasar, wanda ya sanar da hakan yayin amincewa da dokar, wanda ya rattabawa hannu a ranar Litinin, ya ce Najeriya ta yi asarar kimanin jarin dala biliyan 50 na kudaden hannun jari a cikin shekaru 10, wanda rashin tabbas dangane da zartar da kudirin ya haifar.

A cewar shugaban kasar, an dorawa kwamitin alhakin kammala aiwatar da wannan dokar cikin watanni 12.

A saboda haka, ya umarci dukkan ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati da su bayar da cikakken hadin kai don tabbatar da aiwatar da dokar cikin nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: