Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince cewa cigaban Najeriya ya ta’allaka akan harkokin kimiyya da fasaha.

Shugaban kasar yayi jawabi a yau a fadar shugaban kasa dake Abuja lokacin da ya bayar da lambar yabo na shekarun 2020 da 2021 ga wasu ‘yan Najeriya uku wadanda suka yi fice a bangarorin kiwon lafiya da kimiyya.

Wadanda aka bawa lambar yabon sune Dr Oluyinka Olurotimi Olutoye da marigayi Farfesa Charles Ejike Chidume da kuma Farfesa Godwin O. Samuel Ekhaguere.

Shugaban kasar yace tun bayan fara bayar da lambar yabo a Najeriya a shekaru 43 da suka gabata, wadannan sabbin mutane ukun da aka bawa zasu kara yawan wadanda aka bawa lambobin a kasarnan zuwa 79.

Shugaba Buhari, cikin wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar, ya kara da cewa muhimmancin lambar yabon ga habaka cigaban kasarnan baza ta misaltu ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: