Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa kan kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa gomman ‘yan sa kai a Jihar Kebbi

0 138

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa kan kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa gomman ‘yan sa kai a Jihar Kebbi.

Sawaba ta ruwaito yadda ‘yan bindigar suka yi wa ‘yan sa-kai kwanton bauna a karamar hukumar Sakaba ta jihar Kebbi, inda suka kashe akalla 63 daga cikinsu.

‘Yan sa kan sun fito ne daga kauyuka biyar na Takita, Magajiya, Rafin Zuru, Dabai da Sanci.

Shugaban kasar ya bayyana ra’ayinsa ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja.

Ya kuma bayyana wannan mummunar aika aika a matsayin abin ban mamaki, sannan ya yi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi tare da rubanya kokarinsu domin dakile shirin ayyukan ‘yan ta’addan kafin ma su kai hare-hare.

Shugaban kasar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata don magance ‘yan fashi da tsautsayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: