Shugaba Buhari ya bayyana damuwa bisa mummunan kisan da aka yiwa wasu matafiya a jihar Sakkwato

0 77

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa bisa mummunan kisan da aka yiwa wasu matafiya da basu ji ba, basu gani ba a jihar Sokoto.

An bayar da rahoton yadda ‘yan ta’addan, da aka fi sani da ‘yan fashin daji, suka kone akall mutane 37 da ransu a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Matafiyan, wanda suke kokarin yin kaura zuwa wasu sassan kasarnan saboda rashin tsaro a kauyukansu, yan ta’addan sun tsayar da su kimanin kilomita 6 daga garin Sabon Birni.

Da yake mayar da martani dangane da lamarin a jiya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace ya kadu matuka bisa yadda aka kashe mutane, wadanda ke hijira zuwa wani bangare na kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: