Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su bayar da goyon baya ga kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa

0 55

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su ke bayar da goyon baya ga kayayyakin da ake samarwa a cikin kasa domin habaka harkokin kasuwanci da damarmaki a kasarnan.

Ya fadi hakan haka a jiya a jawabinsa wajen bude bikin bajekoli na duniya karo na 35 a Lagos, wanda cibiyar kasuwanci da masana’antu ta Lagos ta shirya.

Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan masana’antu, cinikayya da zuba jari, Otunba Niyi Adebayo, ya bayyana kasuwanci a matsayin ginshikin kawo karshen talauci, da inganta rayuwar mutane, da habaka cigaban tattalin arziki.

Shugaban kasar ya sanar da cewa daya daga cikin manyan kudirorin gwamnatin tarayya shine samar da yanayin da zai bunkasa kasuwanni.

Shugabar cibiyar, Toki Mabogunje, a jawabinta na maraba, tace shirye-shiryen cibiyar da harkokinta da horas da ma’aikata, ana gudanar da su ne domin habaka tattalin arziki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: