Shugaba Buhari ya ce idan ba a magance matsalar tsaro ba tattalin arzikin Najeriya ba zai taba bunkasa ba

0 76

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi imanin cewa idan ba a magance matsalar tsaro ba, tattalin arzikin Najeriya ba zai taba bunkasa ba.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yayin kaddamar da wasu ayyuka.

A jawabinsa na jiya, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da iyakar kokarinta domin ci gaban kasarnan har zuwa watan Mayun 2023, inda ya kara da cewa zai mika mulki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne a wajen kaddamar da kamfanin mai na Oriental da cibiyar karatu daga gida ta Muhammadu Indimi da kuma wata cibiyar taro ta kasa da kasa.

Muhammadu Indimi ne ya gina cibiyar ga jami’ar Maiduguri.

Shugaba Buhari ya kuma kaddamar da makarantar sakandaren tunawa da Tijjani Bolori da kuma gadar sama ta farko a jihar Borno, da shatale-talen kwastan da titin zuwa Gamboru Ngala wadanda gwamnatin jihar ta gina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: