Shugaba Buhari ya ce Najeriya zata duba yiwuwar mayar da hankali kan samun wutar lantarki ta makamashin Nukiliya

0 81

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce Najeriya zata duba yiwuwar mayar da hankali kan samun wutar lantarki ta makamashin Nukiliya domin rage dogaro da man fetur da kuma rage dumamar yanayi.

Cikin wata sanarwar da Kakakinsa Malam Garba Shehu, ya sanyawa hannu, ya ce shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a taron Majalisar Dinkin Duniya na COP26.

A wani Labarin kuma, Shugaba Buhari ya bukaci Kasashe masu arziki su tallafawa matalautan kasashe, domin rage dumamar yanayi.

A cewar Shugaba Buhari, Kasashe masu karfin arziki sunyi wani shiri na rage amfani da itatuwa, a daidai lokacin da suke jiran kasashe masu tasowa suyi wani shiri fiye da su.

Haka kuma, ya yi kira da a tallafawa masu shirye-shiryen yin amfani da mai musamman Gas a kasashe kamar Najeriya wanda take amfani da fannin a matsayin hanyar samun kudaden ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: