Shugaba Buhari ya ce rufe Iyakokin kasar nan da gwamnatinsa tayi ya taimakawa kasar nan

0 85

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce rufe Iyakokin Kasar nan da gwamnatinsa tayi, fiye da shekara 1, ya taimakawa kasar nan.

Gwamnatin tarayya a watan Agusta na shekarar 2019, ta umarci a rufe iyakokin kasar nan, biyo bayan yadda ake shigo da haramtatun kwayoyi, da Makamai da kuma Kayan Amfanin Gona daga kasahen da suke yammacin Afrika.

A watan Disamba na shekarar 2020, ne Shugaba Buhari ya umarci a bude Iyakoki 4 na kasar nan.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Mista Femi Adesina, ya sanyawa hannu, Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Sarauniyar Netherlands Misis Maxima Zorreguieta a birnin New York.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa tayi kokari matuka wajen aiwatar da gine-ginen hanyoyin da sauran kayan more rayuwa.

Mista Adesina ya ce Shugaba Buhari ya bayyana cewa manufar rufe iyakokin shine domin a karfafawa manoma gwiwa, inda ya kara da cewa Najeriya na cigaba da samarda yanayi mai kyau ga masu son zuba Jari a fannin kasuwancin Noma.

A jawabinta, Sarauniyar Netherlands ta yabawa gwamnatin shugaba Buhari bisa matakan da take dauka kan dakile cutar Corona.

Haka kuma, Mai Magana da yawun Sarauniyar Netherlands ya ce kasar zata tallafawa Najeriya musamman a fannin Noma matukar aka samar da hanyoyin sufuri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: