‘Shugaba Buhari ya ceto Najeriya daga durkushewa cikin shekararsa ta farko bayan karbar mulki a 2015’

0 89

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami SAN, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ceto Najeriya daga durkushewa cikin shekararsa ta farko bayan karbar mulki a 2015.

Malami ya ce Buhari ya ceto Najeriya yayin da take shirin rushewa sakamakon karyewar tattalin arziki da sauran matsaloli cikin kankanin lokaci.

Ministan ya bayyana hakan ne cikin wani shiri a Gidan Rediyon Kano ranar Lahadi, inda ya ce tattalin arzikin ya samu mummunan koma baya kafin zuwan Buhari.

Ya ce abin da Buhari ya cimma cikin kankanin lokaci ko kasashen da suka ci gaba ba za su iya ba.

Malami ya ce Shugaba Buhari bai tsaya a nan ba, ya kirkiro shirin N-Power da tallafin Corona, don cire miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci.

Kazalika, game da bangaren tsaro kuwa, Ministan ya ce Buhari ya ceto yankin Arewa maso Gabas, daga ta’addancin Boko Haram.

Sannan, ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro ke aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a Arewa maso Yammacin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: