Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kirayi Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, da ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu da babban mai bayar da shawar kan tattalin arziki, Doyin Salami, zuwa zaman ganawa a fadar shugaban kasa yau da rana.

An tsara shugaban kasar zai gana da su daya bayan daya a lokuta daban-daban kuma zai nemi bayani kan halin da ake ciki yanzu haka a jihar Imo da bangaren wutar lantarki da kuma halin da tattalin arzikin kasarnan ke ciki.

Idan za a iya tunawa dai, shugaban kasar lokacin da yake Allah wa dai da rikice-rikicen da ake fama da shi a jihar Imo bayan lalata dukiya da kadarorin ‘yansanda da gidan George Obiozor, shugaban kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta Ohaneze, ya sha alwashin sake bibiyar halin da ake ciki a tsaron kasarnan.

Shugaba Buhari ya kuma tofa albarkacin bakinsa dangane da yawaitar dauke wutar lantarki, inda ya nemi afuwar ‘yan Najeriya tare da tabbatar da gaggauta kawo sauki a lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: