Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sababbin ministoci bakwai domin maye gurbin wadanda suka sauka da wadanda ya sauke daga kan mukamansu.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan ne ya karanto sunayen sababbin ministocin da Shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zaman da ta yi ranar Talata.

Sabbin ministocin sun hada da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Abia), Ademola Adegoroye (Ondo), Odum Odi (Rivers).

Sauran su ne Goodluck Nnana Opia (Imo) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi ).

Sanata Lawan ya ce nan gaba za su tantance ministocin da aka mika musu domin tabbatar da su ko kuma akasin haka.

A watan Satumbar 2021 ne Shugaba Buhari ya sauke Ministan harkokin Gona, Alhaji Sabo Nanono da Ministan Ma’aikatar Lantarki, Injiniya Saleh Mamman ba tare da bayyana wani dalili ba.

Kazalika a watan jiya ya umarci ministocinsa da ke son tsayawa takarar siyasa su sauka daga mukamansu.

Ya bayar da umarnin ne domin yin biyayya ga dokar kasar da ta bukaci masu rike da mukaman gwamnati su ajiye aiki kafin su tsaya takara.

Ministoci da dama sun sauka daga mukamansa, sai dai daga bisani wasu sun janye inda suka koma bakin aiki.

Ministocin da ba su koma kan kujerunsu ba sun hada da Rotimi Amaechi, tsohon ministan Sufuri; Ogbonnaya Onu, tsohon ministan Kimiyya da Fasaha; Godswill Akpabio, tsohon ministan Neja Delta da kuma Emeka Nwajiuba, tsohon ministan, tsohon karamin ministan Ilimi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: