Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tantance Wasu Mutane 6 Domin Nada Su A Matsayin Kwamishinonin Tarayya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da sake nadin Abike Dabiri Erewa a matsayin shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.
Bukatar ta shugaba Buhari na kunshe cikin wata wasika da aka aikawa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wacce aka karanta a yau yayin zaman majalisar.
A cikin wasikar, Shugaba Buhari, yace nadin yana bisa turbar tandin sashe na 2 karamin sashe na 2 na dokar da ta kafa hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.
Hakazalika, Shugaba Buhari a wata wasikar ta daban da ya aikawa shugaban majalisar dattawa, ya nemi a tabbatar da mutane 6 domin nada su a matsayin kwamishinonin tarayya na hukumar tattara kudaden shiga da rabon arzikin kasa.
Shugaban kasar ya nada Hauwa Aliyu daga jihar Jigawa, Ayogu Eze daga jihar Enugu, Peter Opara daga jihar Imo, Tanko Ayuba Haruna daga jihar Kebbi, Ismaila Mohammed daga jihar Kwara da Kolawole Daniel Abimbola daga jihar Oyo.
Comments are closed.