Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na yin maganin miyagun laifuka da ke haifar da kalubalen tsaro a kasar nan.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a fadar Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, kamar yadda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar.

Shugaba Buhari ya ce ya umurci rundunar sojin kasarnan da sauran jami’an tsaro da su mayar da hankali wajen tunkarar duk wani mutum ko kungiyar da ke zagon kasa a kokarin da ake na samar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a kasarnan.

Shugaban kasar wanda ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Sakkwato kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a baya-bayan nan sakamakon munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa, ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ya cigaba da jajircewa wajen ganin an kawo karshen aikata miyagun laifuka a jihar da sauran sassan kasarnan.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da Sarkin Musulmi sun godewa shugaban kasar bisa ta’aziyyar tare da tabbatar masa da goyon bayansu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: