Shugaba Buhari ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa baza tayi kasa a gwiwa ba har sai an magance kalubalen tsaro

0 78

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa baza tayi kasa a gwiwa ba har sai an magance kalubalen tsaro da take fuskantar a kasarnan.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu, ya fadi hakan ne a wajen bikin kaddamar da wani littafi wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta, da aka gudanar a Abuja.

Yace gwamnatinsa tana assasa hadin kai tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro domin yin aiki tare wajen yaki da aikata laifuka da sauran ayyukan ashsha a kasarnan.

Shugaba Buhari yace an samar da isassun kudade da kayan aiki domin karfafawa sojoji da nufin inganta ayyukansu.

Haka kuma ya yabawa dakarun sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa kokarinsu na yakar laifuka da sauran ayyukan ashsha a kasarnan.

Kazalika, ya jaddada cewa tilas a samu nasara a yaki da rashin tsaro, inda yace dole Najeriya ta zauna lafiya kuma ‘yan Najeriya suyi rayuwa cikin lumana da tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: