Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaba Biden da al’ummar Amurka murnar bikin ranar samun ƴancin kan Amurka.

Shugaba Buhari ya ce yana kuma nuna goyon baya ga gwamnatin shugaba Biden kan yadda ta ke koƙarin magance manyan ƙalubalen da Amurka ke fuskanta da suka haɗa da nuna wariyar launin fata da kuma yaƙi da annobar korona wanda ta addabi Amurka, ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar ta fi yin kisa.

Kazalika, ya bayyana cewa ya na cike da sha’awar yadda gwamnatin Biden ke ƙoƙarin inganta alaƙar Amurka da ƙasashen Afrika da kuma tabbatar da cigaban nahiyar, tare da bayyana fatan hulɗar Amurka da Najeriya za ta ci gaba da bunƙasa domin amfanin mutanen ƙasashen biyu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: