Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojojin kasarnan da su yi amfani da karfi wajen murkushe ’yan bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a Jihar Neja.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a jiya ta ce shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ga helkwatar Tsaro ta Kasa.

Shugaba Buhari ya nanata cewa samar da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowace al’umma kuma ta hanyar bai wa hukumomin tsaro hadin kai ne za a iya kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: