Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta rage hayakin da take fitarwa gabadaya

0 72

shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta rage hayakin da take fitarwa gabadaya zuwa shekarar 2060.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na kasa a taron shugabanni a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Shugaban kasar ya ce cimma burin sauyin yanayi na kasa da na duniya zai bukaci isasshen tallafi na fasaha da kudade ga kasashe masu tasowa.

Shugaba Buhari ya lura cewa saukaka samun kudaden tallafin yanayi ya zama wajibi idan aka yi la’akari da cutar corona wacce ta durkusar da tattalin arzikin kasashe masu tasowa.

Yayin da yake jawabi dangane da komawa amfani da makamashin gas a Najeriya, shugaba Buhari ya bukaci abokan huldar kasa da kasa da su samar da kudaden gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da makamashin iskar gas a Najeriya.

Yayin da yake amincewa da dena fitar da hayaki gabadaya na iya haifar da sauye-sauyen tattalin arziki a dukkan bangarori, shugaba Buhari ya ce zai bukaci samar da muhimman ababen more rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: