Shugaba Buhari ya zama shugaban shirin gina bishiyoyi na koriyar katanga a Afirka

0 78

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zama shugaban shirin gina bishiyoyi na koriyar Katanga a Afirka.

Karamar ministar ma’aikatar muhallahi, Sharon Ikeazor, ta sanar da haka jiya a Abuja.

Wata sanarwa data fito daga hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar, Sagir el Mohammed, yace Najeriya ta karbe shugabancin ne a karshen taron shugabannin shirin gina bishiyoyi na koriyar Katanga a Afirka, karo na 4 da aka gudanar a Abuja.

Sharon Ikeazor ta tunatar da alkawarukan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauka a taron yanayi da aka gudanar watan da ya gabata a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Tace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kyakykyawan fata dangane da burin nahiyar Afrika na farfado da sama da kadada miliyan 100 na kasar noma da ta lalace domin habaka ayyukan gona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: