Labarai

Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a kasarnan ta hanyar zuba jari a bangarori masu muhimmanci cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Ya fadi haka cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a jiya domin taya yaran Najeriya murnar bikin ranar yara ta bana.

Yace gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tukuru wajen bayar da ilimi ga dukkanin yara.

Shugaba Buhari ya bayyana jajircewarsa wajen ganin ana samun cigaba sosai ta hanyar rage yawan yaran da basa zuwa makaranta.

Yace yaran Najeriya sun cancanci samun kasa mafi kyau mai cikakken tsaro, inda zasu cigaba da yin abokai da cakuduwa da juna tare da tafiye-tafiye lami lafiya, da kuma manyan gobe a bangarori daban-daban.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: