Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Riyadh na Kasar Saudi Arabia domin halartar taron Kasuwanci wanda Cibiyar Bunkasa Kasuwanci ta Shirya gudanarwa.

Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, wanda aka rabawa manema labarai a Abuja.

A cewarsa, Shugaba Buhari zai halarci taron karo na biyar, wanda ake saran yan kasuwa daga Najeriya zasu halarci taron domin tattauna hanyoyin da za’a sake bunkasa kasuwanci a Kasashen Duniya.

Cikin Mutanen da zasu yiwa Shugaba Buhari rakiya sun hada da Ministan Ma’aikatar Sadarwa da Bunkasar Tattalin Arziki Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, da Karamin Ministan Ma’aikatar Kasuwanci Zubairu Dada, da Karamin Ministan Arzikin Man Fetur Timipre Sylva, da kuma Mai bawa Kasa Shawara kan tsaro Babagana Munguno.

Malam Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari zai gudanar da Umrah a Madina da Makka kafin ya dawo Najeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: