Shugaba Buhari zai je kasar Habasha domin halartar taron rantsar da Firai Ministan Habasha

0 61

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gobe Lahadi zai je Kasar Habasha domin halartar taron rantsar da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed domin sake yin wa’adi na biyu a ranar Litinin a birnin Addis Ababa.

Mai taimakawa Shugaban Kasa Kan Kafafen Yada Labarai Mista Femi Adesina, shine ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

A cewarsa, shugaba Buhari zai bar Abuja a gobe Lahadi zuwa babban birnin Adis Ababa na kasar Habasha kuma ana sa rai zai gabatar da jawabin fatan alheri a taron rantsuwar.

Haka kuma ya ce daga nan Shugaba Buhari zai halarci liyafar cin abinci tare da sauran shugabannin ƙasashe da suka halarci zaman.

Ministan harkokin ƙasashen waje Mista Geoffery Onyeama da Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar na daga cikin wadanda za su yi wa Shugaba Buhari rakiya.

Kazalika, sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai dawo Abuja a ranar Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: